Dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun kama wata mata ‘yar ƙasar Chadi da ake zargi da safarar hodar iblis, barasa da sauran haramtattun kayayyaki zuwa ga ‘yan ta’adda da ke ɓoye a tsibiran Tafkin Chadi.
An kama wadda ake zargin ne a ranar Alhamis, 9 ga Yuli, 2026, yayin wani samame da dakarun suka gudanar a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin jami’in yaɗa labarai na Hedikwatar Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a shafinsa na X a ranar Juma’a, 10 ga Yuli, 2026.
A cewar Kyaftin Goni, wadda ake zargin mai suna Rachael Samuel, mai shekaru 48, ta fito ne daga Kelo da ke lardin Chari-Baguirmi na Jamhuriyar Chadi.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa ana jigilar haramtattun kayayyakin ne zuwa wasu wurare da ke cikin tsibiran Tafkin Chadi, yankin da aka san ‘yan ta’adda da amfani da shi a matsayin maboyarsu.
Sanarwar ta kara da cewa dakarun sun kwato kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin naira, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
