Hukumar gudanarwar jami’ar Northwest Kano (NWUK) ta sanar da kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan zargin rashin da’a da ya shafi wani ma’aikacin jami’ar, Dr. Nasa’i Muhammad Gwadabe.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar a ranar 10 ga Yulin 2026, bayan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya yi zargin cewa malamin ya yi yunƙurin cin zarafin wata ɗalibar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ta fuskar lalata.
A cewar sanarwar, ana zargin lamarin ya faru ne a tsohon harabar Jami’ar Bayero Kano (BUK).
Jami’ar ta bayyana cewa ta damu matuƙa da zargin, tare da jaddada cewa ba ta amince da duk wani nau’in cin zarafi ta fuskar lalata, cin mutunci ko wani rashin da’a daga ma’aikatanta ko ɗalibanta ba, ko da kuwa a ina ake zargin lamarin ya auku.
Mahukuntan jami’ar sun ce, bisa ƙudirinsu na tabbatar da adalci, gaskiya da bin ƙa’idojin gudanar da aiki, sun kafa kwamitin bincike wanda aka ɗora wa alhakin tantance gaskiyar zargin tare da gabatar da rahotonsa ga jami’ar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, idan binciken ya tabbatar da zargin, jami’ar za ta ɗauki matakin ladabtarwa da ya dace bisa tanade-tanaden dokoki da ƙa’idojinta.
Jami’ar Northwest Kano ta kuma sake jaddada aniyarta na ci gaba da tabbatar da ƙa’idodin ƙwarewa, gaskiya da ɗabi’a nagari, tare da tabbatar da cewa an yi adalci cikin gaskiya da nuna gaskiya.
A ƙarshe, jami’ar ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa jita-jita ko hasashe, tare da bai wa kwamitin binciken damar gudanar da aikinsa har zuwa kammala binciken.
