Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya bukaci a fara amfani da na’urar kaɗa kuri’a a dukkan zaɓuɓɓukan da ake gudanarwa a ƙasar nan.
Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 9 ga Yuli, 2026, yayin ƙaddamar da shirin dabarun shekaru biyar na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM) na shekarun 2026 zuwa 2030, wanda aka gudanar a Kaduna.
Ya ce wannan matsaya ya samo asali ne daga gogewar da ya samu a lokacin da yake matsayin kwamishinan KAD-SIECOM, inda ya kai ziyarce-ziyarcen nazari zuwa ƙasashen China, Brazil da Amurka domin koyon yadda ake amfani da tsarin kaɗa kuri’a na na’ura.
Tun da farko, shugabar KAD-SIECOM, Hajara Mohammed, ta ce shirin dabarun wata muhimmiyar hanya ce ta inganta ayyukan hukumar tare da tabbatar da ƙwarewa, sahihanci da dorewar amincewar al’umma.
Ta bayyana cewa shirin ya yi la’akari da tsofaffi da sababbin ƙalubalen da ke fuskantar gudanar da zaɓe, ciki har da ƙarancin fitowar masu kaɗa kuri’a, matsalolin sufuri da kayan aiki, sauye-sauyen dokoki da kuma buƙatar ƙara gina amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.
