Mai martaba sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta bai wa sarakunan gargajiya ƙarin iko a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa domin su iya taka rawa yadda ya kamata wajen tafiyar da al’amuran al’umma.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro, inda ya jaddada cewa sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma sasanta rikice-rikice a tsakanin al’umma.
Ya ce duk da irin gudunmawar da sarakunan ke bayarwa, rashin tanadin doka da zai ba su cikakken iko yana rage tasirin ayyukansu, musamman a fannin tsaro da zaman lafiya.
Sarkin ya kuma yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su duba yiwuwar sake fasalin kundin tsarin mulki domin bai wa sarakunan gargajiya gurbi mai ƙarfi a tsarin shugabancin ƙasa.
Ya ƙara da cewa sarakunan gargajiya na kusa da al’umma fiye da kowa, don haka suna da damar fahimtar matsalolin jama’a da kuma samar da hanyoyin warware su cikin sauri da hikima
