Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar nan na 2026, da yawansa ya hau ra naira tiriliyan 68.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a cikin wannan adadi za a ware sama da naira tiriliyan 15 domin biyan bashi.
A kasafin kudin an ware sama da naira tiriliyan 15 domin ayyukan gudanarwar yau da kullum, yayin da aka ware sama da naira tiriliyan 32 don gudanar manyan ayyuka a fadin kasar nan.
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kuma buƙaci hukumomin gwamnati dasu tabbatar sun bi wammam ƙa’idar yin gudunar da komai a bayyane, da kuma amfani da kuɗaɗen da aka ware musu ta hanyoyin da suka dace.
Haka kuma sanarwar ta ce shugaban kasar ya ɗage fara aiwatar kasafin kuɗin ƙasar na 2025 zuwa 30 ga watan Yunin 2026.
Tun da farko an tsara fara aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 ɗin a ranar 31 ga watan Maris ɗin da ya gabata.
