Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa ci gaba da tallafawa bangaren noma jihar da yake yi, bayan isowar manyan motocin tirela 33 dauke da takin zamani da gwamnatin tarayya ta samar domin bunkasa noman bana.
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da siyarwa manoman jihar takin zamani wanda gwamnatin sa samar kuma tayi masa ragin kaso 50 cikin 100 kan kowane buhu domin sauƙaƙawa manoma.
Gwamnan ya ce tallafin takin ya zo akan lokaci, kuma wata alama ce ta kudirin gwamnatin tarayya na karfafa harkokin noma da tabbatar da wadatar abinci a fadin Najeriya , kuma gaba kadan gwamnatin Kano zata fasalta yadda za a raba takin domin tabbatar da adalci.
Gwamnan ya kuma godewa Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, bisa ayyukan jin kai da take gudanarwa ga mata, matasa, tsofaffi da manoma a jihar Kano, wanda a cewar sa hakan yana muhimmiyar rawa wajen haɓaka rayuwar su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Ministan Noma da Samar da Abinci na Najeriya Sanata Abubakar Kyari, wanda Dahiru Abbas ya wakilta na cewa nan gaba kadan manoma dubu ashirin da uku da dari takwas a Kano, za su amfana da wasu shirye-shiryen tallafin noma da suka hada da kayan aikin gona da sauran kayayyakin noma.
