Fitaccen mai ƙirƙira a kafafen sada zumunta, Mutari Hamidu, wanda aka fi sani da MK Tecnic, ya ce babban burinsa a yanzu shi ne tabbatar da cewa duk wanda ya kalli bidiyoyinsa ya samu wani darasi da zai amfani rayuwarsa.
MK Tecnic ya bayyana cewa bayan ya shafe lokaci yana ƙirƙirar bidiyoyin nishaɗi, ya fahimci cewa kafafen sada zumunta na bawa masu ƙirƙira damar isar da saƙonni masu amfani ga al’umma.
A cewarsa, wannan ne ya sa ya fara mayar da hankali wajen samar da bidiyoyin da ke ɗauke da saƙonnin ilimantarwa, ƙarfafa kyawawan ɗabi’u da zaburar da matasa su kasance masu tunani mai kyau.
Ya ƙara da cewa saƙonnin da yake samu daga masu bibiyarsa na nuna masa cewa wasu daga cikinsu suna amfana da abubuwan da yake wallafawa, lamarin da ke ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba.
MK Tecnic ya ce zai ci gaba da amfani da kafafen sada zumunta wajen ƙarfafawa mutane gwiwa domin su rungumi kyawawan ɗabi’u masu amfani ga al’umma.
