Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTuhume-tuhumen da yan sanda ke yiwa Mu'az Magaji

Tuhume-tuhumen da yan sanda ke yiwa Mu’az Magaji

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana dalilin da ya sa ‘yan sanda suka cafke tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Mu’azu Magaji.

Yan sandan sun cafke Muaz Magaji ne a Abuja jim kadan bayan kammala hirar kai tsaye da shi a gidan talabijin na Trust da ke Utako Abuja.

Nan take aka kai shi Kano, kuma ya kwana a hedikwatar rundunar da ke Bompai.

Mai Magana da yawun rundunar  Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ‘yan sandan sun kama shi ne bayan da tsohon Kwamishinan ya ki mika kan sa ga ‘yan sanda domin amsa tambayoyi lokacin da aka gayyatace shi.

SP Kiyawa, ya ce ‘yan sandan sun gayyace shi, bisa umarnin kotu na a bincike shi, Amma yaki amsa gayyatar.

“A yanzu haka muna binciken tuhume-tuhumen da ake yi Masa Waɗanda suka hada da bata suna, cin mutunci da gangan, karya da kuma tayar da kalaman da ka iya tayar d hankali,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Idan ba a mantaba Kadaura24 ta rawaito tun a makonni biyu da Suka gabata Muaz Magaji ya wallafa a shafinsa na Facebook Cewa Rundunar Yan Sanda ta Kasa reshen jihar kano ta aike masa da goron gayyata domin ya amsa tambayoyi .

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...