Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGanduje ya umarci sarkin Gaya ya mayar da hankali kan al’amuran tsaro

Ganduje ya umarci sarkin Gaya ya mayar da hankali kan al’amuran tsaro

Date:

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci sabon sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim da ya bashi hadin kai wajen gudanar da mulkinsa, musamman al’amuran da suka shafi tsaro.

Gwamna Ganduje ya bukaci hakanne ya yin bikin bayar da sanda ga sabon sarkin Gaya na 3 mai daraja ta daya da ya gudana ranar Asabar a garin Gaya.

Gwamnan ya ce akwai bukatar sarkin ya kula da al’amrun tsaro, duba da yadda ya zamewa al’umma dan zane, yake kuma ci musu tuwo a kwarya.

Gwamnan ya kuma umarci sarkin da ya hada hannu da hakimai da dagatansa wajen, tabbatar da tsaro a masarautar.

“Lallai ka yi aiki da hakimanka, da dagatai da limamai da duk masu fada aji, wajen ganin an inganta tsaro.

Gwamnan ya kuma ja hankalin sarkin da ya kula da al’amuran ilim, a cewarsa ilimi kyauta ne kuma dole a jihar Kano.

Ya kuma ce dole sarkin ya sanya masu kawo masa rahoto daga cikin hakimai da dagatai na wadanda basu sanya ‘ya’yansu makaranta ba.

Haka zalika gwamnan ya ce dole ne sarkin ya mayar da hankali kan al’amuran noma, musamman a wannan lokaci da ake bukatar wadataccen abninci.

Gwamna Ganduje ya kuma taya sarkin murnar zama Sarkin Gaya na 3 a jerin manyan sarakunta masu daraja ta daya

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories