Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon sanata, Ahmed Mohammed Makarfi, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Makarfi ya bayyana cewa halin da ƙasar ke ciki na rashin tsaro ya kai matakin da ke bukatar daukar matakin gaggawa domin dakile yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen jama’a.
Ya ce idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar za ta ci gaba da tabarbarewa tare da yin barazana ga rayuka, tattalin arziki da zaman lafiya a ƙasar.
Makarfi ya kuma bukaci gwamnati ta ƙara ƙarfafa hukumomin tsaro, tare da samar musu da kayan aiki da dabarun zamani domin tunkarar matsalar cikin inganci.
A cewarsa, Najeriya na buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati da jama’a domin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi sassa da dama na ƙasar.
