Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓensa a zaɓen 2027 a Jihar Kaduna, ranar 24 ga Oktoba, 2026, a cewar Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari.
Yari ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yammacin ranar Juma’a, bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya yi masa bayani kan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen.
Ya ce shugaban ƙasar ne ya buƙaci ganawar domin jin cikakken bayani kan matakin da kwamitin ya kai wajen shirya yaƙin neman zaɓen, da kuma tattauna jadawalin ziyarar da za a kai jihohi daban-daban na ƙasar.
Da yake tsokaci kan yiwuwar nasarar Tinubu a zaɓen 2027, Sanata Yari ya yi watsi da ra’ayin cewa ’yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi, za su iya kayar da shugaban ƙasar.
Yari ya bayyana cewa samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na buƙatar ɗan takara ya samu gagarumin goyon baya daga Arewa da Kudu, yana mai cewa dogaro da goyon bayan yanki guda kaɗai ba lallai ya wadatar wajen samun nasara ba.
