Mukhtar Yahya Usman
Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Lawal, ya ce Bulo Ahmad Tinubu ya tafka babban kuskure wajen zabar musulmi a matsayin mataimakinsa.
Wanan na kunshe cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ga manema labarai.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Lahadi ne Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben da za a yi a shekara mai zuwa 2023.
Lawal ya ce zaben na Shettima ya nuna cewa wasu ‘yan baranda kuma ‘yan amshin-shata ne suka takura Tinubun ya yi haka.
Ya ce bisa ga dukkan alamu, gwamnonin arewa da wasu manyan arewar ne suka sa hakan , da cewa ba za su taba zabar dan takarar da ke da mataimaki Kirista dan arewa ba, kuma shi Tinubun ya yarda da su, in ji Babachir.