Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTinubu ya kaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga magidanta

Tinubu ya kaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga magidanta

Date:

Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga magidanta miliyan 15.

Tinubu ya kaddamar da shirin a yau Talata a bikin ranar kawo karshen talauci ta duniya, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tinubu ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume yayin kaddamar da shirin.

Wannan shiri wani bangare ne na matakan ragewa ‘yan kasa radadi tun bayan janye tallafin man fetur.

A jawabin ta yayin taron ministar ba da agaji, Betta Edu tace za a bai wa kowane magidanci naira 25,000 har na tsawon wata uku.

Ta Kara da cewa akalla yan Najeriyar da zasu ci gajiyar wannan shiri sun Kai miliyan 65 idan aka kirga adadin magidantan da iyalansu.

Latest stories

Related stories