Kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Haruna Aliyu Dangyatin, ya yi kira ga al’ummar Arewa da su goyi bayan sake zaɓen shugaba Tinubu a zaɓen 2027, yana mai cewa shugaban na bin yankin bashin siyasa saboda rawar da ya taka wajen ganin marigayi Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa.
Dangyatin, wanda shi ne mai kula da ƙungiyar City Boy Movement a jihar Jigawa, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar Jahun.
Ya ce nasarar Buhari a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2015 da kuma sake zaɓensa a 2019 ba za ta yiwu ba tare da goyon bayan Tinubu da wasu manyan ’yan siyasar kudu maso yamma ba, saboda haka, a ra’ayinsa, ya kamata arewa ta rama wannan taimako ta hanyar goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027.
Kakakin majalisar ya kuma ce taron masu ruwa da tsaki na APC wani ɓangare ne na shirye-shiryen wayar da kan masu zaɓe da gabatar musu da ’yan takarar jam’iyyar a matakan shugabanci daban-daban gabanin babban zaɓen 2027.
