Gwamnatin Kano ta ce akwai buƙatar a ƙara samun kyakkyawar fahimtar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummar jihar, domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
Kwamshinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin wani wasan ƙwallon ƙafar sada zumunta da gwamnatin Kano ta shirya domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Waiya ya ce wasan an shirya shi ne tsakanin jami’an tsaro daban-daban da matasan da ke ƙarƙashin shirin na gwamnatin Kano me taken Tudun muntsira wato Safe Corridor, domin samar da yanayin sada zumunta tsakanin jami’an tsaro da waɗanda ke cikin shirin, tare da gina amana da kyakkyawar alaƙa tsakaninsu.
Kwamshinan ya ce wasanni na da muhimmiyar rawa wajen haɗa kan al’umma da inganta zaman lafiya, yana mai cewa haɗin kai, fahimtar juna da zaman tare cikin lumana su ne ginshiƙan gina al’umma mai ci gaba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Waiya na cewa, hulɗa mai kyau da waɗanda ke cikin shirin na Safe Corridor na da muhimmanci wajen taimaka musu su koma cikin al’umma yadda ya kamata, su kuma kasance masu amfani ga kansu da sauran jama’a.
