Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiSudan ta dakatar da wasu gidajen Talabijin na kasashen Larabawa yada shirye-shirye...

Sudan ta dakatar da wasu gidajen Talabijin na kasashen Larabawa yada shirye-shirye a kasarta

Date:

Kasar Sudan ta dakatar da wasu gidajen talbijin na kasashen Larabawa guda uku, inda ta zarge su da rahotonin da ba su dace ba da kuma wallafa labarai masu illa.

Gidajen talabijin din sun hada da Sky News Arabia Mallakar Hadaddiyar Daular Larabawa da Al Arabiya da Al Hadath mallakar Saudiyya, wadanda suka yi rahotonni sosai kan yakin basasa da rikicin siyasa a Sudan.

Ministan yada labaran sudan, Graham Abdel Gader, ya ce dakatarwar ta biyo bayan rashin kwarewa da aiki da gaskiya da ake bukata, wajen bayar da rahoto da kuma rashin sabunta lasisinsu.

Dakatar da Sky News Arabia kuma ta samo asali ne daga wallafa rahoton da bai kamata ba, da kuma labarai masu illa a cewar kafofin watsa labarai na cikin gida.

Sai dai gidajen talabijin na Al-Hadath da Al-Arabiya, sun ce ba a sanar da su kan dakatarwar a hukumance ba kuma sun saba sabunta lasisinsu.

Dakatarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta zargi Sky News Arabia da yada wani jabun rahoton yan bindiga.

Tashar ta yi amfani da faifan bidiyon harin da kungiyar Al-Shabab ta kai a Somaliya a shekarar 2016, a wani labari na kungiyoyin yan ta’adda da ake zargin suna yaki tare da sojojin kasar Sudan.

 

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...