Saurari premier Radio
25.1 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAn zabi Najeriya a wadda za ta jagoranci shirin samar da matsugunni...

An zabi Najeriya a wadda za ta jagoranci shirin samar da matsugunni na MDD

Date:

Majalisar Dinkin duniya ta zabi Nigeria a matsayin kasar da zata jagoranci shirin samar da matsugunni na majalisar dinkin duniya wato UN-Habitat.

Manajan shirin na yammacin Africa Mista Mathias spaliviero ne ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci Karamin ministan Gidajen da raya birane na Kasar nan Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a Ofishin sa.

Minista Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bayyana jin dadinsa tare da tabbatar wa manajan shirin cewa Najeriya za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya dace domin cigaba da samun nasarar shirin.

A cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga karamin ministan Adamu Abdullahi ya fitar, yace ministan ya nanata kudurin ma’aikatar wajen samar da tsaro, lafiya, da muhalli mai kyau ga daukacin ‘yan Najeriya.

Tun da farko Manajan shirin UN-Habitat mai kula da yammacin Afirka Mista Mathias Spaliviero ya bayyana cewa kasashe biyu na Kamaru da Kenya sun hakura sun Janye domin Najeriya ta zama shugabar shirin a wannan karon.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...