Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da naɗin tsohon Shugaban Majalisar, Balarabe Sa’idu Gani, da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa, a matsayin kwamishinoni.
Majalisar ta amince da naɗin nasu ne bayan kammala tantance su a zaman majalisar na ranar Talata, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Jibril Isma’il Falgore.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tura sunayen mutanen biyu gaban majalisar domin cike guraben da suka samu a ma’aikatun Yaɗa Labarai da Ma’adinai.
Da yake magana da manema labarai bayan tantance shi, Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya ce zai ba da fifiko wajen farfaɗo da ayyukan kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnatin jihar idan aka naɗa shi Kwamishinan Yaɗa Labarai.
Ya ce, “Babban abin da zan mayar da hankali a kai shi ne farfaɗo da ayyukan Gidan Rediyon Kano, ƙara yawan tashoshin ARTV, da kuma samar da isassun ma’aikata da kayan aikin da suka dace domin jaridar Triumph ta koma wallafa jarida a kullum.”
Bature ya ƙara da cewa ƙarfafa kafafen yaɗa labaran gwamnatin jihar zai inganta ayyukansu wajen yi wa al’ummar Kano hidima.
A nasa ɓangaren, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Isma’il Falgore, ya taya Balarabe Sa’idu Gani murnar samun amincewar gwamna da kuma tabbatar da naɗinsa da majalisar ta yi.
Ya kuma bayyana fatan cewa sabbin kwamishinonin za su sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya kamata.
