Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugabannin ECOWAS na taron gaggawa kan yawan juyin mulki a Afirka ta...

Shugabannin ECOWAS na taron gaggawa kan yawan juyin mulki a Afirka ta yamma

Date:

Shugabannin Kasashen Afirka ta Yamma sun gudanar da wani taron gaggawa a Accra, babban birnin kasar Ghana kan juyin mulkin da ake yawan samu a yankinsu a dan tsakanin nan.

Taron na ranar Alhamis dai na zuwa ne bayan Burkina Faso ta zama kasa ta uku mambar Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da ta fuskanci juyin mulki cikin kasa da shekara biyu.

A makon da ya gabata ne dai sojoji suka hambarar da gwamnatin Shugaba Christian Kabore na Burkina Faso a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar rikice-rikice.

Kasar ta biyo bayan Mali ne wacce ita ma aka yi juyin mulkin a watan Mayun 2020, sai kuma kasar Guinea wacce ita ma aka hambarar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde a watan Satumban bara.

Kazalika, tattaunawar na zuwa ne ’yan kwanaki bayan wani yunkuri na kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoco Embalo a Guinea-Bissau wanda bai yi nasara ba.

Lamarin dai ya jefa tsoro a zukatan shugabannin yankin, a kokarinsu na daidaita al’amura a cikinsa.

Hankula dai a yanzu sun koma wajen ganin matakin da shugabannin za su dauka wajen yi wa tufkar hanci, saboda kar matsalar ta bazu zuwa ragowar kasashen.

Ana sa ran kungiyar ta ECOWAS ta tattauna yiwuwar kakaba wa kasar ta Burkina Faso sabon takunkumi, kari a kan dakatarwar da ta yi mata tun da farko.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da Burkina Faso daga kwamitinta na zaman lafiya

Latest stories

Related stories