Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabu shiga aji ranar Litinin a BUK-ASUU

Babu shiga aji ranar Litinin a BUK-ASUU

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kugiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU a jami’ar Bayero ta ayyana ranar Litinin 7 ga Fabrairu a matsayin ranar da ba za a gudanar da karatu a jami’ar ba.

PREMIER RADIO ta ruwaito wannan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Haruna Musa da sakatarensaYusuf Madugu suka sanyawa hannu da yammacin ranar Alhamis.

Kungiyar ta ce a maimakon kin shiga ajin za ta yi amfani da damar wajen wayarwada kan dalibai irin halin da gwamnatin tarayya ta jefa su a ciki na kin biyansu hakkokinsu.

A cewarsu har yanzu gwamnatin tarayya ta ki cika alkawuran da ta daukarmusu duk da cewa an lallabasu aka hanasu tafiya yajin aiki.

Idan za a iya tunawa dai tun a watan Disambar bara ne kungiyar ta ASUU ta yi yunkurin tafiya yajin aiki amma aka lallabasu suka hakura, bisa alkawarin za a biya musu bukatunsu.

Sai dai a cewar kungiyar tun bayan da aka lallabasun har yanzu gwanatin taki sauraron su ballantana ta cika alkawuran da ta dauka.

A don hakan ne kungiyar taga dacewar ta tattauna da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki musamman iyayen yara wajen sanar da su halin da ake ciki.

Haka kuma tana fatan iyayen yaran da daliban ba za su zargesu ba da zarar sun yi yunkuri komawa yajin aikin.

Latest stories

Related stories