Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar CPC ta gano inda ake hada gurbataccen mai a Kano

Hukumar CPC ta gano inda ake hada gurbataccen mai a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usaman

Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki ta jihar Kano, Consumer Protection Council (CPC) ta ce ta gano wurin da ake hada gurbataccen man girki.

Premier Radio ta ruwaito shugaban hukumar Idris Bello Danbazau ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Misbahu Yakasai ya raba wa manema labarai a Kano.

Danbazau ya ce bankado wurin na daga cikin kokarin da hukumar ke yi na kare jama’a daga amfani da gurbatattun kayayyaki.

An dai gano wirinne a yanin Dakata Rinji, da ke karamar hukumar Nasarawa, a cikin birnin Kano.

A cewarsa, wurin da ake tace man  na kusa da wata katuwar bola da galibin al’ummar yankin a nan suke zubar da shara.

Ya bayyana cewa wurin ba shi da tsafta kuma yana da hadari ga lafiyar jama’a.

“KSCPC ba ta nufin rage daraja ko lalata kasuwancin wani, ana yin hakan ne domin kawo gyara.

“Wannan zai inganta kasuwancinsu harma ga masu amfani da su don siyan samfurori na yau da kullun,” in ji MD.

Shima da yake nasa jawabin, Daraktan tabbatar da inganci na majalisar, Dokta Tijjani Jafaru, ya bayyana cewa majalisar ta samu rahoton sirri ne  a ranar Larabar da ta gabata, game da wurin da ake hada gurbataccen man.

A cewarsa basu yi wata wata ba suka kai ziyara wurin don ganewa idanun su abinda ake yi a wurin.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da marawa hukumar baya domin cimma manufofinta.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...