24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiSheikh Ibrahim Khalil ya koma Jam'iyyar ADC

Sheikh Ibrahim Khalil ya koma Jam’iyyar ADC

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen malamin addinin musuluncin a jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil, ya koma jam’iyyar ADC.

Shugaban jam’iyyar ta ADC na jihar Kano Shuaibu Ungogo ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau juma’a.

Shuaibu Ungogo ya ce malamin ya shiga jam’iyyar ne tare da Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa tare da wasu shehunnan Malaman jami’a guda 8 domin ceto jihar Kano daga halin da ta tsinci kan ta.

Haka kuma shugaban na ADC ya ce nan gaba kaɗan jami’yyar za ta shirya taron karɓar Shehin Malamin tare da sauran waɗanda su ka shigo Jami’yyar.

Sheikh Ibrahim Khalil wanda shi ne shugaban majalisar malamai a Kano ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a shekarar 2021 a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikici tsakanin ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Latest stories