33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKaramar hukumar Dawakin Tofa ta haramta zancen dare

Karamar hukumar Dawakin Tofa ta haramta zancen dare

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

Majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa ta haramta zancen dare tsakanin samari da ‘yan mata da ke Shirin yin aure a yankin.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Ado Tambai Kwa ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar makon jiya.

Matakin ya biyo bayan umarnin da masarautar Bichi ta bayar na dakatar da zancen daren a yankin.

Ya ce daga yanzu duk wani saurayi da ke son zuwa zance wajen budurwarsa, to sai ya fara aika magabatansa wurin iyayenta.

Ya kara da cewa dole nevsu gudanar da gwajin jini bayan amincewar iyayen na ya nemi ‘yarsu domin tabbatar da cewa basa dauke da wata cuta da za ta haramta aure a tsakaninsu.

Haka kuma majalisar ta kafa dokar rage kayan lefe, zuwa akwati uku kacal, kafin aure.

Sanarwar ta gargadi dagatai da masu unguwanni da su tabbatar an dabbaka dokar, a cewarta kaucewa umarnin na jawowa dagaci ko mai unguwa rasa mukaminsa.

Baya ga hana zancen daren majalisar ta kuma haramta kidan DJ, inda kuma masu yin majalisi za su nemi izinin hukumar Hisbah kafin su gudanar da majalisinsu.

Latest stories