Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari ya ƙaddamar da shirin rage haihuwa a Najeriya

Buhari ya ƙaddamar da shirin rage haihuwa a Najeriya

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon tsari kan yawan jama’a don ci gaba mai dorewa a kasar nan.

Shugaban ya ƙaddamar da wannan shiri ne a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Shugaban ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan ƙaruwar da ake samu na haihuwa ta hanyar faɗaɗa shirye-shiryen samar da hanyoyin bayar da tazarar haihuwa na zamani a faɗin ƙasar.

Domin tabbatar da wannan tsarin, shugaban ya kafa wani kwamiti da zai riƙa sa ido kan yawan jama’a wanda shi da kansa zai jagoranta.

Haka kuma mataimakinsa zai ci gaba da taimaka masa a wannan ɓangare sannan akwai shugabannin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnatin a matsayin mambobi.

Shugaba Buhari ya ce babban burin wannan shiri shi ne inganta rayuwar duka ‘yan Najeriya wanda hakan na daga cikin abin da gwamnatin ƙasar ke son cimmawa.

Buhari ya ce ƴan Najeriya sun fi kowace al’umma yawa a nahiyar Afrika kuma ita ce ta bakwai a duniya baki ɗaya kuma tana daga cikin ƙasashe ƙalilan na duniya da ake ƙara samun haihuwa sosai

Shi ma shugaban hukumar ƙidayawa ta kasa Nasir Isa Kwarra ya buƙaci yan Najeriya su rungumi tsare-tsaren da gwamnatin ta fitar kan batun haihuwa.

Isa Kwarra ya bayyana cewa an samar da  sabon shirin ne bayan tuntuɓa daga masu ruwa da tsaki da kuma ƙungiyoyin da lamarin ya shafa a faɗin kasar  nan.

Wani jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya Matthias Schmale, ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa wannan tsarin da Shugaba Buhari ya ƙaddamar zai yi nasara sakamakon dalilai da dama.

Hakazalika ya jinjina wa gwamnatin kasar nan kan ƙaddamar da shirin inda ya ce duniya baki ɗaya da Majalisar Ɗinkin Duniya na sa ran ganin Najeriya ta zama ƙasar da za a samu raguwa a fannin mutuwar ƙananan yara da raguwar samun ciki da ƙananan yara mata ke yi da haihuwa.

Haka kuma ya ce ana sa ran samun raguwa a yawan haihuwa baki ɗaya da ƙara rungumar hanyoyin bayar da tazarar haihuwa na zamani.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...