24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKano da Sokoto basu da shugaba-Cewar jam'iyyar APC

Kano da Sokoto basu da shugaba-Cewar jam’iyyar APC

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Makwanni uku kafin babban taron jam’iyyar APC na kasa, jam’iyyar ta fitar da sunayen shugabanninta a matakin jihohi amma banda Kano da Sokoto.

PREMIER RADIO ta ruwaito jam’iyyar ta kaddamar da shugabannin jihohi 34 a wani taro da ta gudanar ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

A na ganin dai kin kaddamar da shugabannin a jihohin Kano da Sokoto ba ya rasa nasaba da rikicin cikin gida da jam’iyyun ke fama da su a jihohinsu.

Idan za a iya tunawa dai a jihar Kano an gudanar da zaben shugabancin jam’iyyar guda biyu tsakanin tsagin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma na Malam Ibrahim Shekarau.

Zabukan sun gudana a wurare mabanbanta inda tsagin gwamnan Kano suka zabi Abudullahi Abbas, ya yin da tsagin Shekarau suka zabi Ahmad Haruna Zago.

Sai dai uwar jam’iyyar kawo yanzu bata karbi zaben kowanne bangare ba, la’akari da cewa maganar tana kotu.

Shugabannin a sauran jihohi.

Shugabannin da aka fitar a matakin jihohin sun hadar da Dr. Kingsley Ononogbu (Abia), Alh Ibrahim Bilal (Adamawa), Mr Augustine Enefiok Ekanem (Akwa Ibom), Hon Basil Ejike (Anambra), Alh Babayo Aliyu Misau (Bauchi), Dr. Dennis Otiotio (Bayelsa), Mr Augustine Agada  (Benue), Hon.  Ali Bukar Dalori (Borno), da Mr. Alphonsus Orgar Eba Esq.  (Cross River).

Sai kuma Dattijo Omeni Sabotie (Delta), Hon.  Stanley Okoro Emegha (Ebonyi), Col David Imuse (Edo) mai ritaya, Barr.  Omotosho Paul Ayodele (Ekiti), Chief Ogochukwu Agballah (Enugu), Mr Nitte K Amangal (Gombe), Dr Macdonald Ebere (Imo), Hon.  Aminu Sani Gumel (Jigawa), Air Cdre Emmanuel Jekada (Rtd) (Kaduna), Alh.  Muhammad Sani (Katsina), Alh.  Abubakar Muhammed Kana (Kebbi) da Hon.  Abdullahi Bello (Kogi).

Sauran su ne Prince Sunday Adeniran Fagbemi (Kwara), Hon.  Cornelius Ojelabi (Lagos), Mr John D Mamman (Nasarawa), Hon.  Haliru Zakari Jikantoro (Niger), Chief Yemi Sanusi (Ogun), Engr Ade Adetimehin (Ondo), Prince Adegboyega Famodun (Osun), Hon Isaac Omodewu (Oyo), Hon Rufus Bature (Plateau), Chief Emeka Turanci (Rivers).  Hon Ibrahim Tukur El-Sudi (Taraba), Alh Muhammed A. Gadaka (Yobe), Alh.  Tukur Umar Danfulani (Zamfara) da Alh.  Abdulmalik Usman (FCT).

Latest stories