Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban hukumar Hisbah na a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce...

Shugaban hukumar Hisbah na a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce za a yi kidan ƙwarya da na shantu domin nishaɗantar da zawarawan da za yi bikinsu a Jihar.

Date:

Shugaban hukumar Hisbah na a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce za a yi kidan ƙwarya da na shantu domin nishaɗantar da zawarawan da za yi bikinsu a Jihar.

Sheikh Daurawa ya fadi hakan ne lokacin da yake karin haske a kan shirye-shiryen aurar da zawarawa da ’yan mata 1,800 da gwamnatin Kano ke shirin yi.
A cewar Sheikh Daurawa, za a yi shagulgula iri-iri domin nishadantar da ma’auratan, tun da a cewarsa, addinin Musulunci bai hana ba.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Hisbah ta warewa kowacce daga cikin Ƙananan Hukumomin Kano 44 Naira dubu 500 domin shagulgulan nishadi a yayin biki, adadin kudin da ya kai Naira miliyan 22.
Gwamnatin Kano dai ta ware sama da miliyan 800 domin bikin zawarawan.
har zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta sanar da ranar da za a yi bikin ba, amma ta ce tana ci gaba da shirye-shirye.

Latest stories

Related stories