Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin inganta fannin kimiyya da fasaha...

Gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin inganta fannin kimiyya da fasaha domin ci gaban al’ummar jihar kano ta ko wacce fuska.

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin inganta fannin kimiyya da fasaha domin ci gaban al’ummar jihar kano ta ko wacce fuskata.
Kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha na kano Muhammed Tajo Othman ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci babban sakataren ma’aikatar da sauran daraktocin ma’aikatar zuwa ziyarar gani da ido a cibiyoyin addinin musulunci na kananan hukumomin Kura da Wudil a jihar Kano domin duba wasu injinan wasan kwallon kafa da aka yi watsi da su a baya.
Kwamishinan ya bayyana cewa, makasudin ziyarar shi ne duba yadda za a sake farfado da injinan ta yadda za a cigaba da aikin dasu domin tafiya dai dai da zamani kamar yadaa ake buga harkokin wasanni a fadin duniya.
Da suke nasu jawabin wasu daga cikin mazauna kananan hukumomin da kwaminishinan ya ziyarce su, sun bayyana cewa injinan na iya samar da kayan da zasu gudanar kwallon kafa guda dari a duk rana guda wanda kuma kananan hukumomi 44 kano zasu amfana da wajen.
A wani labarin kuma, Kwamishina ya kai ziyarar duba hukumar tattara bayanai ta gwamnatin jihar Kano, dake sakatariyar Audu Bako a wanoi bangare na shirye-shiryen mika ayyukan hukumar ga ma’aikatar kimiyya da fasaha ta jihar kano.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...