Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiSarkin Musulmi,ya umarci al’umma da su soma duban watan Muharram na Sabuwar...

Sarkin Musulmi,ya umarci al’umma da su soma duban watan Muharram na Sabuwar Shekarar musulunci ta 1446 Hijiriyya daga yau Jumu’a.

Date:

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’umma da su soma duban watan Muharram na Sabuwar Shekarar musulunci ta 1446 Hijiriyya daga yau Jumu’a 5 ga watan Yuli, 2024.

A madadin Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Masarautar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, ne ya fitar da sanarwar.

Farfesa Sambo, ya ce duk wanda ya samu ganin watan ya sanar da Majalisar Sarkin Musulmi ko wani uban kasa ko hakimi domin sanar da al’umma.

Watan Muharram shi ne watan farko a tsarin watanni 12 na Shekarar musulunci.
Idan an ga watan, Asabar 6 ga watan Yuli, 2024, zai kasance ranar farko a shekarar 1446 Hijiriyya.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...