Saurari premier Radio
30.7 C
Kano
Monday, July 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKeir Starmer yayi nasara da kuri'a mafi rinjaye a zaben Birtaniya.

Keir Starmer yayi nasara da kuri’a mafi rinjaye a zaben Birtaniya.

Date:

Sakamakon zaben na Birtaniya na nuna cewar Firaministan kasar Rishi Sunak ya gaza kaiwa ga nasarar da yake hankoro, babban dan adawa na jamiyyar Labour Keir Starmer ya yi nasara da gagarumin rinjaye.

A wani abun mamaki tuni Firaministan Birtaniya mai barin gado Rishi Sunak ya sanar da amincewarsa da shan kaye a wannan zabe, inda ya kira Firaminista mai jiran gado Keir Starmer domin fada masa cewar ya amince da shan kaye a zaben.

Tuni jamiyyar Labour ta samu kujeru 394, ita kuwa Conservative ta samu 103, jamiyyar Liberal Democrat ta samu kujeru 63 da sauran jamiyyu suka raba kujeru 40 a tskaninsu, ana kuma dakon sakamakon kujeru 51.

Tuni Satrmer ya bayyana jin dadinsa da samun wannan nasara.

Wasu daga cikin shugabannin duniya kamar firaministan Australian Anthony Albanese sun fara taya firaministan mai jiran gado murnar lashe wannan zaben.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...