Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa Ali Khamenei, wanda ya mutu a hare-haren Isra’ila da Amurka a ranar farko ta yaƙin.
A wani saƙo da aka wallafa da sunansa domin godewa waɗanda suka halarci jana’izar mahaifinsa, Mojtaba Khamenei ya ce za su ɗauki fansar jininsa da kuma na sauran waɗanda suka mutu a harin da Amurka da Isra’ila suka kai wanda ya bayyana a matsayin kisan gilla.
Ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan fansa buri ne na al’ummar Iran, yana mai cewa dole ne a tabbatar an aiwatar da ita ba tare da gazawa ba.
Tun dai bayan da aka ce ya maye gurbin mahaifinsa a matsayin jagoran Iran, Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama’a ba, kuma har yanzu ba a ji saƙon murya ko na bidiyo daga gare shi ba, sai dai rubuce-rubucen da ake wallafawa da sunansa.
