Dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar New Democratic Congress (NDC), Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi kira ga dukkan ‘yan ƙasa da suka cancanci yin rajistar zaɓe amma har yanzu ba su yi ba,
musamman matasa da mata, da su yi amfani da sabon tsarin rajistar zaɓe ta intanet na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), su yi rajista daga gidajensu ta amfani da lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) kafin wa’adin ranar 24 ga Yuli, 2026.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Asabar, Kwamared Gwarzo ya bayyana cewa INEC ta ƙaddamar da sabon dandalin rajistar kai tsaye ta intanet, wanda ke bai wa masu yin rajista karo na farko damar fara da kammala rajistarsu ta hanyar shiga shafin cvr.inecnigeria.org.
Ya jaddada cewa kaɗa ƙuri’a wata muhimmiyar hanya ce da ‘yan ƙasa ke bayyana ra’ayoyinsu tare da ba da gudunmawa wajen tsara makomar dimokuraɗiyyar ƙasa.
A cewarsa “Wannan sabon tsari ya kawo ƙarshen wahalar tsayawa dogayen layuka. Yanzu matasanmu, iyaye mata da ‘yan’uwanmu mata za su iya yin rajista daga gida ta amfani da wayoyinsu ko kwamfutocinsu. Babu wani uzuri na rashin shiga cikin tsarin dimokuraɗiyya.”
Gwarzo ya yi kira na musamman ga matasa da mata da su fito su yi rajista, yana mai jaddada cewa Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) shi ne babban makamin kawo sauyi mai kyau.
Ya ce “PVC ɗinku shi ne ƙarfinku. Shi ne makamin da za mu yi amfani da shi wajen kawo sauyi mai kyau ga iyalanmu, al’ummominmu da kuma Jihar Kano baki ɗaya. Ina kira musamman ga matasa da mata—ku yi rajista, ku karɓi katin zaɓenku, sannan ku fito ku zaɓa a shekarar 2027.”
Dan takarar na NDC ya kuma bukaci dukkan ‘yan Najeriya da suka cancanci yin rajista amma ba su yi ba da su kammala rajistarsu ta farko ta intanet, su je cibiyoyin da INEC ta tanada domin ɗaukar bayanan tantancewa (biometric), sannan su karɓi katin PVC ɗinsu da zarar an kammala.
Ya ƙara da cewa “Makomar Jihar Kano da Najeriya tana hannun ‘yan ƙasa masu wayewa da ɗaukar alhakin da ya rataya a wuyansu. Ku yi rajista tun yanzu, ku fito ku yi zaɓe cikin lumana a shekarar 2027, domin tare mu gina Kano irin wadda muke buri.”
Haka kuma Gwarzo ya yi kira ga shugabannin al’umma, malamai da ƙungiyoyin addini, ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin fararen hula da su haɗa kai wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa su su yi rajistar zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
