Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar yan sanda ta garagadi yan kwadago su guji tada tarzoma yayin...

Rundunar yan sanda ta garagadi yan kwadago su guji tada tarzoma yayin zanga-zanga

Date:

Babban sufeton ƴan sandan kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun yace ƴan sanda ba za su lamunci duk wani abu da zai kawo rikici ba yayin zanga-zangar da gamayyar kungiyoyin kwadago ta kasa NLC zata gabatar a gobe Laraba.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce ƴan ƙasa suna da ƴancin yin zanga-zanga kamar yadda kundin mulki ya tanada amma dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ƴan sandan ta ce a baya irin wannan zanga-zanga tana rikiɗewa ta zama tashin hankali, saboda haka ta ke gargaɗin cewa ba za ta bari a gudanar da duk wani abu da zai kawo matsalar tsaro ba.

ACP Adejobi ya ce duk wani yunƙurin tayar da rikici a lokacin zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago zai fuskanci fushin hukuma.

Ƙungiyoyin ƙwadago a kasarnan sun shirya fara zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewa da soke tallafin manfetur da gwamnatin tarayya tayi.

Latest stories

Related stories