Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin APC:Ganduje, Shekarau sun nemi a raba mukaman Jam'iyya

Rikicin APC:Ganduje, Shekarau sun nemi a raba mukaman Jam’iyya

Date:

Mukhtar Yahya Usman

A jiya Juma’a ne dai kwamitin sulhun rikicin jam’iyar APC a Kano, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na APC na Ƙasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sake zaman sulhunta tsakanin ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Premier Radio ta rawaito cewa a zaman da a ka yi na ranar Talatar da ta gabata, Ganduje bai halarta ba bai kuma tura wakili ba.
Majiyoyi sun ce gwamnan ya ƙi halartar zaman ne sabo da ya na da yaƙinin samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara, bayan da wata Babbar Kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɗan takarar sa na shugabancin jam’iya na jiha, Abdullahi Abbas.

Kwatsam kuma sai ga gwamnan a zaman na jiya Juma’a bayan da a ranar Alhamis, kwamitin riƙo na jam’iyar ya rantsar da shugabannin jam’iya na jiha a jihohi 34, amma ban da Kano da Sokoto.

A zaman sulhun dai na jiya, wanda a ka kwashe awanni shida a na gabzawa, ba a cimma matsaya ba.

Sai dai kuma kowanne ɓangare ya miƙa kundin buƙatarsa ta yadda ya kamata a kasafta muƙaman jam’iya ga shugaban kwamitin, Buni.

Kwamitin kuma zai yi nazari a kan buƙatun da kuma kasafta muƙaman, inda da ga bisani za a sake kiran zaman a shaidawa ɓangarori biyun irin kasafin muƙaman da kwamitin ya yi.

Amma wasu majiyoyi da su ke cikin zaman sulhun sun tabbatar da cewa zai yi wuya duka ɓangarori biyun su amince da kasafi

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...