Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiRikicin makiyaya da manoma ya haddasa zaman dar-dar a Makoda

Rikicin makiyaya da manoma ya haddasa zaman dar-dar a Makoda

Date:

Rahotonni daga karamar hukumar Makoda na bayyana cewa ana zaman dar-dar sakamakon wani rikici daya kaure tsakanin fulani da manoma wanda ya yi sanadiyyar jikkata wasu mazauna yankin.

Tun da fari dai wata Akuya ce mallakin wasu fulani dake kauyen Warba ta shiga gonar wani babba a Makoda, ta yi masa barna inda shi kuma ya kama akuyar ya kaita kauyen domin ya shaida musu irin barnar da ta yi masa tare da rokon su, su kula da dabbobinsu ta yadda ba za su ci gaba da yi musu barna ba.

Rahotanni sun ce akwai wata yarjejeniya da akayi tun a baya tsakanin fulanin garin na Warba da kuma manoma dake garin Makoda, cewa fulanin ba za su bari dabbobinsu su shiga gonakin manoman ba su yi musu ta’adi, sai dai a wannan karon akuyar ta shiga gonar daya daga cikinsu wanda hakan ya saba da yarjejeniyar da su ka yi.

Wannan dai ya fusata Fulanin inda cece-kuce ya barke tsakaninsu, wanda har ya kai ga sun lakadawa wannan manomi daya mayar musu da akuyar duka, abin da ya tilasta shi kiran yan uwansa daga Makoda domin kawo masa dauki.

Bayan manoma daga makoda sun kawo masa dauki rigima ta kaure tsakanin fulanin na kauyen warba da manoma daga makoda har ta kai ga an jikkata wasu mutane Shida wanda yanzu haka suna kwance a asibiti.

To sai dai an samu rashin fahimta wanda har ta kai ga yanzu haka ba’a jituwa kuma al’ummar wannan yanki suna zaman dar-dar sakamakon hatsaniya da har yanzu ke ci gaba da afkuwa.

Har kawo wannan lokaci dai rundunar yan sandan Kano ba ta ce komai ba dangane da wannan batu.

Ku bibiyemu a labaranmu na gaba zamu kawo muku cikakken rahoton kan halin da ake ciki.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...