Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin APC: Buhari ya mayarwa da Tinubu martani

Rikicin APC: Buhari ya mayarwa da Tinubu martani

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Fadar shugaban kasa ta mayar wa da Bola Ahmad Tinubu martani kan kalaman sa na cewa in ba dan shi ba da Buhari bai kai labari a zaben da ya gabata ba.

A cewar fadar babu wanda ya isa ya ce shi kaɗai ya yi uwa ya yi makarɓiya har Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulki a zaɓen 2015.

Mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ne ya fitar da sanarwa a shafinsa na twitter da yammacin ranar Litinin.

Ya ce abin da ya wuce a baya bai kamata ya zama abin da za a yi la’akari da shi ba  wurin zaɓen da ke tafe.

Ya bayyana cewa abin da ke da muhimmanci a yanzu shi ne a zaɓi shugaba da zai kawo ci gaba a Najeriya.

Ya bayyana cewa akwai waɗanda suka ba shugaban shawara da ya ƙara takara da waɗanda suka gina jam’iyya inda ya ce babu wani mutum guda da zai iya cewa shi ya yi duka waɗannan shi kaɗai.

Sai dai ana ganin sanarwar ba ta rasa nasaba da wasu kalamai da Bola Ahmed Tinubun ya yi masu kama da gori inda ya ce shi ya taimaka Buhari ya ci zaɓe

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories