Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBaba Impossible ya caccaki Ganduje kan ziyartar Murtala Garo

Baba Impossible ya caccaki Ganduje kan ziyartar Murtala Garo

Date:

Kwamishinan al’amuran addinai na Kano Muhammad Tahar Adam ya caccaki Gwamna Ganduje kan ziyarar da ya kaiwa Shekarau da Murtala Sule Garo.

Kwamishinan ya bayyana Hakan ne yayin taron manema Labarai da ya gudanar yau Alhamis.

A cewarsa ko kadan bai Kamata gwamnan ya je gidan Garon ba, Inda ya ce Kamata yayi Shi Murtala ya je Inda gwamnan ya ke.

Ana ganin dai Ganduje ya kaiwa Murtala Sule Garo ziyara ne domin ya lallashe shi kan yunkurinsa na ficewa daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP.

Rahotonni sun ce Murtala Sule Garo ya shiga taking saka da gwamnan ne tun bayan da ya janyewa Sanata Barau takarar Sanatan Kano ta Arewa.

Ka zalika A kwanakin baya Ganduje ya kai ziyara ga Sanata Shekarau wanda ya sauya sheka zuwa NNPP a jiya.

“Neman Sulhu abu ne mai kyau, mussaman mutumin da kake gani idan an rabu za a samu nakasu.

‘Amma a matsayinsa na mai girma gwamna da irin yadda yake abu ne mai kyau ace shi da kansa yaje.

“Amma idan mutum zai je wurin da bazai yi amfani ba, da muguwar rawa gara kin tashi.

“Misali ya tashi ya je wajen Sanata Ibrahim Shekarau ay zuwan bai yi kyau ba saboda mutane sun yi ihu, kuma abinda aka tafi nema a wurinsa don ya hakura ba ayi ba, kaga wannan abu ne wanda bamu ji dadi ba”.

Latest stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...