Saurari premier Radio
37.8 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBadaru kaji tsoron Allah wajen fidda dan takara-Farouk Adamu Aliyu

Badaru kaji tsoron Allah wajen fidda dan takara-Farouk Adamu Aliyu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Dan takarar gwamnan Jigawa a jam’iyyar APC Farouk Adamu Aliyu ya roki gwamnan jihar Muhammadu Badaru Abukar ya ji tsoron Allah wajen fitar da dan takara.

Farouk Adamu Aliyu ya roki gwamnan ne yayin taron ayyana takararsa ta neman gwamnan Jigawa ranar Laraba.

Ya ce akwai bukatar gwamnan ya sanya tsoron Allah ya kuma tabbatar ya bada dama anyi zaben fidda gwani tsakani da Allah.

Da yake kaddamar da takarar tasa, Adamu Aliyu ya ce idan aka zabeshi gwamnan Jigawa zai mayar da hankali wajen inganta harkar ilimi a jihar.

A cewarsa zai dora daga Inda gwamna mai barin vado ya tsaya don ciyar da al’ummar jihar gaba.

Dan takarar gwamnan ya ce ya lura jihar Jigawa na fuskantar yawan mace-macen mata yayin haihuwa.

Ya ce matukar aka bashi dama zai kawo karshen wannan matsala

“Duk da cewa gwamnati mai barin gado tayi kokari wajen harkar lafiya, amma akwai matsalar mutuwar mata lokacin haihuwa.

“Wannan matsalar ta dame mu kuma za mu tabbatar mun kawo karshenta.” Ya ce.

Haka zalika Farouk Adamu Aliyu ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen bunkasa harkar Noma.

Ya ce duk da cewa jihar Jigawa na da kasar noma Amma har yanzu ana yi mata kallon talakar jiha a kasar nan.

A cewarsa ya zama dole a duba harkar Noma a kuma ingantata domin ceto jihar daga kankin talauci

Ya kuma yabawa gwamann jihar Jigawa Muhammad Badaru Abukar kan ayyukan da ya gudanar a jihar.

Inda ya yi alkawarin zai dora daga Inda gwamnan ya tsaya domin ciyar da jihar gaba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...