24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin KanoGanduje ya baiwa shugaban ma'aikatan Kano rikon ofishin Ali Haruna Makoda

Ganduje ya baiwa shugaban ma’aikatan Kano rikon ofishin Ali Haruna Makoda

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Karibullah Abdulhamid Namadobi 

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa shugaban ma’aikatan Kano, Usman Bala umarnin ci gaba da kula da ayyukan ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Ali Haruna Makoda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa NNPP mai alamar kayan marmari da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Muhammad Garba ya fitar ya ce shugaban ma’aikatan na Kano zai ci gaba da kula da ayyukan ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano har zuwa lokacin da za a nada wani a mukamin.

A cikin sanarwar gwamna Ganduje ya yi fatan Usman Bala zai yi aiki tukuru don tabbatar da komai ya tafi yadda ya dace a ofishin na shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.

Latest stories