Premier Radio 102.7 FM
Labarai Siyasa

Ba mu zabi Ahmad Lawan ya zama Dan takara ba-APC

Mukhtar Yahya Usman

Jam’iyyar APC ta karyata labarin da ke yawo cewa ta zabi shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.

Kwamitin Gudanarwa na Kasa na Jam’iyyar APC (NWC) ne ya sanar da haka a yammacin ranar Litinin.

Jam’iyyar ta sanar da hakan ne bayan bullar wani labari da ke cewa ta zabi Ahmad Lawan a matsayin dan takara tilo, a yayin da ake shirin gudanar da zaben dan takarar shugaban jam’iyyar a ranar Talata.

Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sulaiman Argungu ya ce labarin kanzon kurege ne ake yadawa game da daukar Ahmad Lawan.

Ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar daga yankin Arewa da kuma Kudu sun yi ittifaki cewa a bai wa dan yankin Kudu takarar, don haka babu yadda za a yi sabanin hakan.

A yanzu dai jam’iyyar ta tashi haikan wajen ganin ta fitar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 ta hanyar masalaha, babu hamayya.

Daliget 2, 340 ne dai za su kada kuri’ar zaben fitar da dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 a ranar Talata.

A Wani Labarin...

Manchester United na son daukar Robert Lewandowski

Aminu Abdullahi Ibrahim

NNPP ta zabi Doguwa a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar

Mukhtar Yahya Usman

Buni ba zai sake zama shugaban APC ba-El-Rufai

Mukhtar Yahya Usman