Matatar Dangote ta sanar da rage farashin fetur da dizal da take sayar wa masu sayen kayayyaki a manyan kaya, a wani mataki da ta ce zai taimaka wajen rage tsadar makamashi da sauƙaƙa rayuwar al’umma.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, kamfanin ya bayyana cewa ya rage farashin litar fetur daga Naira 1,215 zuwa Naira 1,165, wanda ke nuna ragin Naira 50 a kowace lita.
Haka kuma, matatar ta rage farashin litar dizal daga Naira 1,650 zuwa Naira 1,570, inda aka samu ragin Naira 80 kan kowace lita.
Kamfanin ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarinsa na rage tsadar man fetur, da sauƙaƙa farashin kayayyaki ga masu amfani da su, tare da tallafa wa ci gaban harkokin kasuwanci a sassa daban-daban na Najeriya.
A cewar matatar, rage farashin ya sake nuna aniyarta ta ci gaba da samar wa ‘yan Najeriya ingantattun kayayyakin man fetur a farashi mai sauƙi.
Matatar ta kara da cewa za ta ci gaba da tabbatar da wadatar mai, tare da inganta ayyukanta domin biyan bukatun jama’a, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki.
Matatar Dangote ta ƙara da cewa idan yanayin kasuwa ya ci gaba da ba da dama, za ta sake duba farashinta domin masu amfani da man fetur su ci gaba da cin gajiyar ragin farashi.
