Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiPutin ya zargi kasashen yamma da haifar da rikice-rikicen da ake gani...

Putin ya zargi kasashen yamma da haifar da rikice-rikicen da ake gani a sassan duniya.

Date:

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zargi kasashen yamma da haifar da rikice-rikicen da ake gani a sassan duniya, har ma ya yi gargadin cewa a shirye kasar take da tayi amfani da makaman nukiliya wajen bawa kanta kariya.

Shugaban mai shekaru 71 na bayyana hakan ne a wurin bikin tunawa da nasarar da kasarsa ta samu kan Jamus a lokacin yakin duniya na biyu.

Shugaban yayin taron da suka yi a dandalin Red Square da ke birnin Moscow ya ce manyan kasashen yammacin duniya sun manta da rawar da Tarayyar Soviet ta taka wajen fatattakar ‘yan Nazi, amma kuma suke ci gaba da kitsa rikici a duniya.

Jawabin Putin ya zo ne a daidai lokacin da dakarun Rasha ke samun ci gaba a yakinta da Ukraine da kuma rantsuwar wa’adi na biyar da ba a taba ganin irinsa ba bayan da ya lashe zaben shugaban kasa ba tare da ‘yan adawa ba.

A shekarar da ta gabata Rasha ta bayyana ficewarta daga yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya da kuma yarjejeniyar rage yawan makamai da ta kulla da Amurka.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...