Rundunar ƴan sandan Kano ta kama wani da ake zargi da safarar buhunhuna 18 da ke dauke da kunshi 879 na ganyen da ake zargin tabar wiwi ce a kauyen ƴan Shado da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano.
Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Juma’a, 15 ga Mayun 2026.
Ya ce, jami’an ‘yan sanda a Dawakin Tofa sun kama mutumin mai suna Umaru wanda aka fi sani da Jalo, yayin da yake sauke buhunhunan ganyen da ake zargin tabar wiwi ce zuwa cikin gidansa.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci a gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda ke da hannu wajen safarar.
Sanarwar ta kuma ce, rundunar ta kuma bukaci al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai kan masu aikata laifi.
