Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiPDP a Kaduna ta bukaci majalisar jihar da ta binciki gwamnatin El-rufa'i...

PDP a Kaduna ta bukaci majalisar jihar da ta binciki gwamnatin El-rufa’i kan yadda ta kashe kuɗaɗenta.

Date:

Jamiyyar PDP a jihar Kaduna ta bukaci kwamitin da majalisar jihar ta kafa domin bincikar yadda tsohuwar gwamnatin malam Nasir el-rufai ta kasha kudadenta, da ta fadada bincike har zuwa batun korar ma’aikatan jihar sama da 27,000 da El-rufain yayi batare da biyansu hakkokinsu ba.

Sakataren yada labarai na jamiyyar Alberah Catoh ne ya bayyana haka, inda ya koka kan yadda tsohuwar gwamnatin taci mutuncin ma’aikata a wancan lokaci.

Wannan dai na kunshe cikin jawabin ranar ma’aikata ta duniya da jamiyyar ta fitar a yau Talata inda jamiyyar ta nuna alhini kan halin da m,a’aikatan jihar ke ciki.

Idan za a iya tunawa dai gwamnatin malam Nasiru Elrufa’i ta kori dubban ma’aikata yawancinsu malaman makarantun firamare da sakandire saboda zargin kasa cin jarrabawar da gwamnatin ta shirya musu.

Abinda ya jawo cece kuce da tada kura tsakanin kungiyoyin ma’aikata da gwamnatin jihar.

 

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...