Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya sanar da cewa yana sa ran ƙaddamar da aikin bututun iskar gas na Ajaokuta,Kaduna da Kano (AKK) a watan Satumban shekarar nan, bayan da aikin ya kai matakin ƙarshe.
Mai magana da yawun kamfanin, Andy Odeh, ya bayyana cewa aikin ya kai kashi 98 cikin 100, inda aka riga aka kammala shimfiɗa bututun iskar gas daga Ajaokuta da ke Jihar Kogi har zuwa Kano.
Ya ce a halin yanzu, ana mayar da hankali ne kan kammala muhimman ayyukan da ke saman ƙasa, waɗanda suka haɗa da cibiyoyin karɓa da sa ido kan zirga-zirgar iskar gas, kafin a fara amfani da bututun a hukumance.
Sai dai NNPCL ta bayyana cewa har yanzu ba a ayyana takamaiman ranar da za a fara amfani da bututun ba, duk da cewa ana sa ran ƙaddamar da shi a watan Satumba.
An fara aikin bututun iskar gas na AKK ne a shekarar 2020, amma duk da shafe kusan shekara shida ana aiwatar da shi da kuma alƙawuran da aka yi a baya na kammala shi, har yanzu aikin bai fara aiki gaba ɗaya ba.
