Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta lalata miyagun ƙwayoyi masu nauyin kimanin tan 12.234, waɗanda aka kama a sassa daban-daban na jihar Kano da kuma Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
An gudanar da aikin ne a ranar Litinin karkashin jagorancin Kwamandan NDLEA na Kano, Dahiru Yahaya Lawal, a matsayin wani ɓangare na shirin yaki da sha miyagun kwayoyi.
Miyagun ƙwayoyin da aka lalata sun haɗa da tabar wiwi, heroin, cocaine, tramadol, codeine, methamphetamine da sauran ƙwayoyi masu sa maye.
Hukumar ta ce an ƙwace su ne ta hanyar ayyukan leƙen asiri da samame na musamman, sannan kotuna suka ba da umarnin a lalata su.
NDLEA ta ce bincike ya gano cewa masu fataucin miyagun ƙwayoyi na amfani da ramuka da koguna da ke yankin Rimin Kebe domin ɓoye kayansu, lamarin da ya nuna yadda suke ƙoƙarin kauce wa jami’an tsaro.
Hukumar ta kuma bayyana cewa tun daga watan Janairun 2026, ta kama mutane 904, ciki har da maza 869 da mata 35.
Haka kuma ta ƙwace fiye da tan 2.5 na miyagun ƙwayoyi, tare da samun hukuncin kotu kan mutane sama da 54, inda wasu aka yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru har 15.
Da yake jawabi a madadin Shugaban NDLEA, Daraktan Ayyuka da Bincike, DCGN Ahmed Suleiman Ningi, ya ce lalata miyagun ƙwayoyin a bainar jama’a wata alama ce da ke nuna cewa doka na aiki, kuma saƙo ne ga masu fataucin miyagun ƙwayoyi cewa ba za a lamunci ayyukansu ba.
