Saurari premier Radio
35 C
Kano
Friday, April 12, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNajeriya za ta kashe naira biliyan uku wajen kwaso 'yan ƙasar nan...

Najeriya za ta kashe naira biliyan uku wajen kwaso ‘yan ƙasar nan daga Ukraine

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe dala miliyan takwas da rabi – fiye da naira biliyan uku – wajen aikin kwashe ‘yan ƙasar  nan daga ƙasashe huɗu maƙotan Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi a can.

Ma’aikatar harkokin waje da haɗin gwiwar ta agaji ne za su gudanar da aikin kwashe ‘yan ƙasar kusan 5,000 daga ƙasashen Poland da Ramania da Slovakia da Hungary.

Ƙaramin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya faɗa wa manema labarai a yau Laraba jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa cewa za a tura jirage uku don gudanar da aikin.

Jiragen sun ƙunshi na kamfanin Air Peace biyu da kuma na Max Air ɗaya.

Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen ta ce za a fara gudanar da aikin ɗebo su bayan sun tsallaka maƙota daga Ukraine sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin dakarun Rasha da na ƙasar.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories