Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaNAFDAC ta gargadi yan kasar nan dangane da ajiye dafaffen abinci sama...

NAFDAC ta gargadi yan kasar nan dangane da ajiye dafaffen abinci sama da kwana uku a cikin firiji.

Date:

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAFDAC ta gargadi yan kasar nan dangane da ajiye dafaffen abinci sama da kwana uku a cikin firiji.

Da take gargadin yayin jawabi a taron ranar kula da amincin abinci ta duniya, babbar daraktar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce ajiye abinci a cikin firji na tsawon kwanaki zai iya sawa kwayoyin cuta su gurbata abincin wanda hakan zai iya janyo rashin lafiyar da za ta iya ajalin mutum.

Ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar samar da abinci da su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da ingancin abinci da kuma kawar da duk wata barazana da za ta iya janyo hatsari game da ingancin abinci.

Ta bayyana cewa akwai rawar da kowa zai iya takawa domin tabbatar da ingancin abinci tun daga masu samar da shi zuwa masu cin sa.

A wata sanarwa da mai bayar da shawara kan harkokin yada labarai na hukumar, Sayo Akintola ya fitar, hukumar lafiya ta duniya WHO ta kiyasta cewa, a duniya daya daga cikin mutum 10 na fama da rashin lafiya, kuma dubu 420 ke mutuwa a kowace shekara saboda cin gurbataccen abinci.

TRT

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...