Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaba Vladimir Putin, na Rasha ya isa Hanoi babban birnin Vietnam a...

Shugaba Vladimir Putin, na Rasha ya isa Hanoi babban birnin Vietnam a zagaye na biyu.

Date:

Shugaba Vladimir Putin, na Rasha ya isa Hanoi babban birnin Vietnam a zagaye na biyu, na ziyarar da yake yi a gabashin Asiya, a abin da ake ganin wata alama ce ta goyon bayan da Rasha ke samu a yankin.

Mista Putin zai gana da sabon shugaban kasar ta Vietnam, To Lam, da sauran shugabannin jam’iyyar Kwaminisanci.

Amurka, na nuna rashin jin daɗinta game da ziyarar, tana cewa bai kamata wata kasa ta sama wa Mista Putin wani dandalin tallata yaƙin da yake yi a Ukraine ba.

A jiya Laraba ne Putin ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar tsaro da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, a ziyararsa ta farko a Pyongyang fiye da shekara ashirin.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...