Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMutane 30 sun bata sanadiyar kifewar kwale-kwale a Anambra

Mutane 30 sun bata sanadiyar kifewar kwale-kwale a Anambra

Date:

Kimanin mutane 30 sun bata yayin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji 85 ya kife a garin Umunnankwo da ke karamar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.

 

Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar data gabata.

 

Wata majiya ta bayyana cewar kwale-kwalen ya taso ne daga gadar Onukwu inda ya nufi kasuwannin Nkwo da Ogbakuba; duka a karamar hukumar Ogbaru, lokacin da ya kife.

 

Shaidan gani da ido ya ce kawo yanzu ba’a gano mutane 30 ba daga cikin wadanda suka fada ruwan.

 

Da yake tsokaci kan lamarin, shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Ogbaru, Hon. Pascal Aniegbuna, ya tabbatar da faruwar alamarin a yau Asabar.

 

Ya Kuma bayyana cewa tuni an ceto wasu daga cikin fasinjojin yayin da wasu da dama suka rasa rayukansu.

 

Latest stories

Related stories