Saurari premier Radio
22.5 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMuna buƙatar gwamnatin tarayyata ta soke wasu ma'aikatun gwamnati - Sanata Godswill...

Muna buƙatar gwamnatin tarayyata ta soke wasu ma’aikatun gwamnati – Sanata Godswill Akpabio

Date:

Shugaban Majalisar dattawan Sanata Godswill Akpabio ya buƙaci gwamnatin tarayyata ta soke wasu ma’aikatun gwamnati, sannan ta yi garambawul a wasu, ta yadda za a samu ingantuwar aiki.

Yayin da yake jawabi jim-kadan kafin shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a zauren majalisar, Sanata Akpabio ya ce hakan zai tabbatar da an gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Shugaban Majalisar dattawan ya shawarci gwamnati ta duba hanyoyin rage basukan da ta gada daga tsahuwar gwamnati.

Sanata Akpabio ya kuma bayyana cewa majalisa za ta bai wa ɓangaren zartarwa haɗin kai domin aiwatar da kasafin kuɗin yadda ya dace

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...